Jami’ar Gwamnatin tarayya dake Dutsinma (FUDMA) dake jihar Katsina arewa maso yammacin Najeriya ta kammala dukkanin shirye shirye domin gudanar da bikin yayen dalibanta karo na bakwai (7) da na takwas (8).
Za’ a gudanar da bikin ne a matsugunin jami’ar dake garin Dutsinma, Karamar hukumar Dutsinma, jihar Katsina.
Mataimakin shugaban jami’an wato Vice Chancellor, Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi shine ya bayyana hakan ga manema labarai dangane da shirye shiryen bikin da jami’ar keyi na yaye daliban tare da karrama manyan mutanen.
Farfesa Bichi yace a lokacin bikin wanda zai gudana a ranar asabar 2 ga watan Disambar nan, jami’ar zata yaye dalibai masu digirin farko su 4365 wadanda daga cikin su dalibai 112 sun kammala karatun ne da sakamako mai daraja ta daya sai kuma guda 1131 wadanda suka kammala da sakamako mai daraja ta biyu, mai babba da kaddamar daraja, yayin da guda 646 su kuma suka kammala da sakamako mai daraja ta ukku.
Mataimakin shugaban jami’ar ya kuma bayyana cewa a karon farko jami’ar zata yi bikin yaye dalibai masu babban digiri na biyu da na ukku su 401 wadanda daga cikin su dalibai 11 ne suka kammala digirin na ukku sai masu digiri na biyu su 243 a bangare daban daban, yana mai cewa akwai kuma wadanda suka kammala babbar diploma su 149
Yace daliban da suka yi fice wajen samun sakamako mai daraja ta daya zasu karbi kyaututtuka a lokacin bikin.
Farfesa Bichi ya kuma bayyana cewa a lokacin bikin, jami’ar zata karrama wasu manyan mutane da digirin girmamawa
Yace daga cikin wadanda za’a karrama a lokacin bikin akwai tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema da mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar Farouk da kuma mai Martaba Sarkin Bichi a jihar Kano, Alhaji Nasiru Ado Bayero.
Kamilu Lawal.
Leave a Reply