Take a fresh look at your lifestyle.

Cocoa: Manoma 68,000 A Najeriya Za Su Ci Gajiyar Sa Hannun Amurka

118

Akalla manoma 68,000 na Najeriya a jihohin Abia, Cross River, Ekiti, Akwa Ibom, Ondo da Osun za su ci gajiyar sa hannun Amurka a sarkar darajar kokon kasar.

 

Shirin samar da ci gaba na Ma’aikatar Aikin Gona ta Amurka ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar biyo bayan yarjejeniyar hadin gwiwa da kungiyar Lutheran World Relief domin karfafa noman koko a Najeriya.

 

Sanarwar ta bayyana cewa, shirin na dalar Amurka miliyan 22, za a aiwatar da shi cikin shekaru biyar masu zuwa.

 

Da yake jawabi, mai ba da shawara kan harkokin noma, Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya, Dr. Gerald Smith, ya sanar da cewa, aikin zai shafi manoma a yankunan da ba su da fa’ida, amma kuma akwai kyakkyawan fata.

“Manufar ita ce a kara yawan amfanin koko ta hanyar yin amfani da matakan noma masu wayo.

 

“Aikin zai tallafawa ingantattun hanyoyin samun bayanai, albarkatun fasaha da iya aiki, sarrafa bayan girbi da kasuwannin fitar da kayayyaki.

 

“Aikin zai yi amfani da tsarin da zai baiwa manoma damar samar da koko mai yawa da kuma adana albarkatu na kasa da halittu,” in ji Smith.

Comments are closed.