Gwamnan jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya karbi rahoton kwamitin yin rajistar Makarantun Tsangayu a jihar, a ranar Talata.
Gwamna Zulum, ya lura cewar,” Matukar aka fara aiwatar da tsarin koyar da Sana’o’in hannu, tare da sanya tsarin karatun Zamani irin na Boko, ta yadda za’a rika koyar da Darussan Turanci, Lissafi, tare da ilimin nazarin zamantakewa.
Ya ce” babu shakka yin hakan zai basu daman samun takardun shiga Makarantun gaba da Sakandare na Jami’o, Kwalejojin Ilimi da na Kimiyya da Fasaha, don yin karatun dipuloma, Digiri ko kuma N.C.E, kuma yin hakan zai taimaka wajen rage yawan barace-barace a Manyan hanyoyi, da lungunan jihar.”
Tun da farko, Shugaban Hukumar kula da Makarantun Tsangayun jihar Sheikh Khalifa Ali Arabi Abulfatahi, ya bayyana cewar ” Hukumarsa ta kammala yin rajistar daukacin Makarantun Tsangayun jihar a Yankunan Kananan Hukumomi 27 da ke fadin jihar, in banda Kananan Hukumomin Kala-Balge, Guzamala, da kuma Abadam, saboda matsalar rashin tsaron da ya addabi Yankunan.
Ya ce Hukumarsu ta yi rajistar Cibiyoyin Makarantun Tsangayu guda dubu 2, 775, tare da Malamansu har dubu 12, 309, a ya yin da yawan Daluban suka kasance dubu 224, 068.
Ya ce: “a cikin dubu 224, 068, dubu 128, 789, suna Makarantar jeka ka dawone, a ya yin da Dalubai dubu 97, 279 suke kwana a makarantun Tsangayun.”
Leave a Reply