Take a fresh look at your lifestyle.

‘Yan Sanda Sun Gano Gawarwakin Masu Hakar Ma’adinai a Afirka ta Kudu

Usman Lawal Saulawa

0 263

Rundunar ‘yan sandan kasar Afrika ta Kudu ta gano gawarwaki 19 da ake zargin na masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a garin Krugersdorp da ke yammacin birnin Johannesburg.

 

Rundunar ‘yan sandan ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce tana amsa kira ne biyo bayan gano gawarwakin da aka yi a daya daga cikin mahakar ma’adanai da ke yankin.

 

Sun ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa, “an koma da wadanda suka mutu aka ajiye su inda aka gano su”.

 

Rahoton ya ce babu tabbas kan yadda wadanda ake zargin masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba suka mutu, kodayake ‘yan sandan sun ce ba su yi zargin wani abu ba.

 

A halin da ake ciki, sun ce za a yi gwajin gawarwakin mutane domin gano musabbabin mutuwar.

 

Dubban masu hakar ma’adinai da ba su da rajista suna aiki a cikin kasar don neman ma’adinan da ba’a yi amfani da su ba.

 

Dama akan samun yawaitar hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Afirka ta Kudu, inda masu hakar ma’adinai da aka fi sani da suna “zama zamas” suna neman zinarai a yawancin ma’adinan da aka yi watsi da su a ciki da wajen yankin Johannesburg. Krugersdorp gari ne mai haƙar ma’adinai a gefen yammacin Johannesburg.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *