Nan Ba Da Dadewa Ba Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Tashar Daukar Kaya A Filin Jirgin Sama Na Abuja
Abdulkarim Rabiu, Abuja
Ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, ya ce nan ba da dadewa ba shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kaddamar da daya daga cikin ayyukan gina tashashin dakon kaya guda biyu a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin sufurin jiragen sama domin kare matsayin aiwatar da kasafin 2022 da kuma kudirin kasafin kudin 2023 a Abuja.
Ya kuma ce nan ba da dadewa ba Najeriya za ta samu jirgin fasinja na kasa, wanda a halin yanzu yana kan hanyarsa kuma za a kaddamar da shi da tare da jirgi sama samfurin Boeing 737.
Sanata Sirika, ya bayyana cewa kamfanin jirgin zai fara maida hankali ne kan ayyukan jigilar fasinjoji a cikin gida kafin ya yi la’akari da wani aiki na kasa da kasa.
A cewar ministan, fannin sufurin jiragen sama ya samu ci gaba sosai a zamanin wannan gwamnati.
Sirika ya ce a yanzu filayen tashi da saukar jiragen sama sun sami ingantaccen tsaro, yana mai jaddada cewa an samu gagarumar nasara a harkar sufurin jiragen sama na cikin gida a kasar.
“Wannan gagarumin ci gaban ya samo asalili ne sakamakon tsarin da muke samarwa. Filayen jiragen samanmu sun samu sabbin kayayyaki musamman na Legas, Abuja, Kano, da Fatakwal da dai sauransu,” in ji Sirika.
Ministan ya kuma sanar da cewa, za a binciki kwangiloli na na gina tashar daukar kaya wato Cargo da ‘yan kwangilar suka yi watsi da su, sannan a gurfanar da wadanda suka aikata laifin tare da kwato kudaden.
Da yake na sa jawabin Shugaban kwamitin, Mista Nnolim Nnaji, ya ce nan da ‘yan makwanni masu zuwa ne kwamitin zai fara sa ido kan tashoshin jiragen sama na kasa da kasa guda uku da ake sa ran sayarwa da Yan kasuwa hannun jari.
“Kwamitin ya bayyana matukar damuwa da watsi da daya daga cikin muhimman hukumomin tsaro na ma’aikatar, wato hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya,” in ji Hon Nnaji.
Ya kara da cewa kwamitin zai tabbatar da cewa an gyara matsalar tare da yin kira ga ministan da ya fayyace lamarin.
Abdulkarim/Ladan
Leave a Reply