Take a fresh look at your lifestyle.

NIPC Za Ta Taimakawa Najeriya Rage Dogaro Da Mai – Saratu Umar

Abdulkarim Rabiu, Abuja

0 334

Sakatariyar zartaswa kuma babbar jami’ar hukumar bunkasa zuba hannun jari ta Najeriya (NIPC) Uwargida Saratu Umar ta jaddada kudirin hukumar na janyo hankulan kasashen waje don zuba jari kai tsaye ga tattalin arzikin Najeriya.

Sakatariyar zartarwar ta NIPC ta bayyana hakan ne a lokacin da hukumar ke kare kasafin kudin shekarar 2023 a gaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kasuwanci da zuba jari a Abuja.

Har ila ya ta nemi goyon bayan majalisar kasa wajen ganin hukumar NIPC na gudanar da ayyukanta daidai da sauran hukumomi takwarorinta a fadin duniya.

Saratu ta ci gaba da cewa, tare da goyon bayan Majalisar Dokoki ta kasa Hukumar za ta taka rawar gani wajen jawo hankulan masu zuba jari kai tsaye daga kasashen waje zuwa Najeriya ta yadda za a rage dogaro kan Man Fetur tare da tabbatar da cewa an karkatar da zuba jari zuwa wasu sassan da ba na mai ba domin samar da kudaden shiga.

Tun da farko Shugaban Kwamitin Sanata Sa’idu Alkali da wasu ‘yan kwamitin suka bayyana cewa Majalisar Dattawa za ta ci gaba da tabbatar da sa ido ga daukacin hukumomin gwamnatin tarayya domin tabbatar da suna gudanar da ayyukansu yadda yakamata.

Kwamitin ya kuma yabawa hukumar karkashin jagorancin Uwargida Saratu Umar bisa hangen nesanta ga hukumar duk da cewa ba ta wuce ‘yan watanni da nadawa ba.

 

Abdulkarim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *