Rundunar ‘yan sandan farin kaya ta NSCDC reshen jihar Sokoto, ta ce ta ceto mutane hudu da aka yi garkuwa da su tare da kama wani Abdulfatai Adeyemi, kan wannan haramtacciyar hanya.
Kwamandan rundunar na jiha Muhammad Saleh Dada ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ofishin jihar dake Sokoto.
A cewar Kwamandan, an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su Sadiya
Akinyola, Monsurat Adebayo, Halima da Aisha Akinlola dukkansu ‘yan kasa da shekaru daga yankin Kudu maso Yamma na kasar nan, an ceto su ne a babbar tashar mota ta Sakkwato a ranar 28 ga watan Oktoba, 2022.
Ya kara da cewa, binciken farko da jami’an rundunar da ke da alhakin safarar mutane suka gudanar ya nuna cewa wadanda abin ya shafa sun nufi jamhuriyar Nijar ta kan iyakar Illela.
“Mista Abdulfatai Adeyemi ya karbi ‘yan matan hudu daga wani Alpha daya a jihar Legas don taimaka masa ya kai su ga wani a Sakkwato kuma aka ba shi lambar waya ya kira ya mika musu.
“Idan mutum ya karbe su, zai koma kan iyakar illela don hawan sama zuwa makoma ta karshe ta Jamhuriyar Nijar,” in ji shi.
Dada ya ci gaba da cewa, rundunarsa za ta tuntubi jami’an tsaron farin kaya da na Civil Defence na jihar Legas domin tabbatar da cafke wani mutum Alpha.
Ya bayyana cewa da zarar an kammala bincike, za a mika wadanda abin ya shafa ga hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP).
Ya ce al’amuran safarar yara na kara kamari a kasar nan, amma hukumarsa za ta ci gaba da hada hannu da duk hukumomin da abin ya shafa domin rage matsalar zuwa wani mataki mafi karanci a jihar.
Kwamandan jihar ya bukaci iyaye da su rika kula da ‘ya’yansu a matsayin baiwar da Allah ya yi musu kada su yi kasada da rayuwarsu ta hanyar da ba su dace ba.
Leave a Reply