Take a fresh look at your lifestyle.

‘Yan Kasar Mali Sun Yaba Da Matakin Afuwa Ga Sojojin Ivory Coast

Aisha Yahaya, Lagos

0 24

A ranar Juma’a shugaban mulkin sojan Mali Kanar Assimi Goita ya yi afuwa ga dukkan sojojin Ivory Coast 49, wadanda  aka kama a watan Yuli da ya  haifar da dambarwar diflomasiya, kuma ‘yan kasar Mali sun yaba da matakin.

 

 

“Mun dade muna cikin rudanin diflomasiyya, don haka shugaba Assimi Goïta ya samu damar yin afuwa ga wadannan sojoji 49, ina ganin hakan ya kawo sauki ga al’ummar duniya, al’ummomin yankin da kuma daukacin al’ummar Mali da na Ivory Coast,” in ji Zafara Ongoïba.

 

 

Sojojin sun koma gida ne a daren ranar Asabar, kuma a halin yanzu hankali ya kwanta  tsakanin kasashen.

 

 

“Wannan kwanciyar hankali ne. Ganin cewa, Mali da Cote d’Ivoire sun fito daga ƙasa ɗaya. A zahiri muna da al’adu iri daya, amma idan irin wannan abu ya faru, a gare ni ya kamata a daidaita shi cikin aminci amma ba ta hanyar da za ta iya haifar da rashin fahimta tsakanin kasashen biyu ba. Ina tsammanin yana da kyau, an yi shi da kyau, “in ji Malick Sabé.

 

 

Shugaban mulkin sojan Mali ya yanke shawarar yin afuwa ga daukacin sojojin Ivory Coast 49 a ranar Juma’a domin magance tashe-tashen hankula da ke tsakanin Mali da Ivory Coast.

 

 

“Kanar Assimi Goita… yayi afuwa tare akan yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga ‘yan Ivory Coast 49 da kotun shari’a na Mali ya yanke,” in ji wata sanarwa daga mai magana da yawun gwamnati, Kanar Abdoulaye Maiga, ministan kula da yankuna da raba gari.

 

 

A ranar 30 ga watan Disamba, an yanke wa sojoji 46 hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari, yayin da wasu mata uku daga cikin 49 na asali, wadanda aka saki a farkon watan Satumba, aka yanke musu hukuncin kisa ba sa nan.

 

 

An same su da laifin kai hari da makarkashiya ga gwamnati da kuma neman kawo cikas ga tsaron jihar, in ji mai shigar da kara na gwamnati Ladji Sara a wata sanarwa a lokacin.

 

 

An gudanar da shari’ar a Bamako babban birnin kasar a ranar 29 ga watan Disamba shekarar 2022,kuma aka kammala washegari.

 

 

Shari’ar kotun ta zo ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da wa’adin ranar 1 ga watan Janairu da shugabannin kungiyar ECOWAS suka sanya wa Mali na su saki sojojin ko kuma su fuskanci takunkumi.

 

 

Rundunar sojan Mali ta ayyana sojojin, wadanda aka tsare bayan sun isa filin jirgin saman Bamako a ranar 10 ga watan Yuli, a matsayin sojojin haya.

 

 

Ivory Coast da Majalisar Dinkin Duniya sun ce an kai sojojin ne domin samar da tsaro na yau da kullun ga tawagar wanar da Zaman lafiya ta Majalisar Dunkoin Duniya MDD a Mali.

Leave A Reply

Your email address will not be published.