Kasar Senegal Ta Na Zaman Makoki Na Kasa Bayan Hadarin Mota Da Ya Kashe Mutane Da Dama
Maimuna Kassim Tukur
Mutane talatin da takwas sun mutu yayin da wasu suka jikkata a tsakiyar kasar Senegal bayan da wasu motocin Safa-Safa guda biyu suka yi karo a ranar Lahadi, in ji Shugaba Macky Sall a cikin wata sanarwa.
Hatsarin,na daga cikin mafi muni da aka taba tunawa a wannan kasa ta yammacin Afirka, ya kasance yana daya daga cikin manyan wurare daga gabas da yamma kusa da garin Kaffrine, mai tazarar kilomita 220 (mil 137) kudu maso gabashin Dakar babban birnin kasar.
Sall ya fada a shafinsa na Twitter cewa “ya yi matukar bakin ciki” da afkuwar hatsarin kuma ya sanar da zaman makoki na kwanaki uku daga ranar Litinin. Hatsarin ya afku ne bayan da tayar motar bas guda daya ta tashi, inda ta aike ta cikin hanyar wata motar bas da ta nufo ta wata hanya, a wata sanarwa daga mai gabatar da kara na yankin.
Hotunan da aka yi ta yadawa ta yanar gizo sun nuna fararen bas guda biyu, da sukayi karo da Juna.
Hatsarin mota ya zama ruwan dare a kasar Senegal, inda manyan motoci da bas-bas, wadanda galibi sun tsofa da nauyi fiye da kima da kuma jeri, suka yi sanadiyar lalacewar titunan da haifar da ramuka da gudun wuce sa’a.
A shekarar 2017, wasu bas guda biyu sun yi karo da juna, inda mutane 25 suka mutu, ciki har da wasu da ke kan hanyarsu ta zuwa wani biki na addini.
Leave a Reply