Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gayyato Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma ,Ministan makamashi, Abubakar Aliyu, da Babban mai bada shawara akan tattalin arziki, Farfesa Doyin Salami, domin gana wa da Shugaban kasa a fadar shi dake Abuja .
Tattaunawar ta kasance ne akan halin da Jihar Imo ke ciki,da kuma halin da harkokin samar da wutar lantarki da tattalin arziki suke ciki
Za’a iya tunawa shugaban kasa yayi tir da rikici da lalata kayayyaki da rusa gidaje har da samar kayan ‘Yan sanda da gidan shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo farfesa George Obiozor, kuma yayi alkawarin sake duba halin tsaro a kudu maso gabashin Najeriya..
Hakazalika Shugaba Buhari ya nuna rashin jin dadin shi game da irin halin karancin hasken wutar lantarki da yaki ci yake cinyewa,ya baiwa ‘yan Najeriya hakuri tare da alkawarta shawo kan matsalar.
LADAN NASIDI
Leave a Reply