Take a fresh look at your lifestyle.

Sabuwar Shekarar Sinawa: Najeriya Ta Taya kasar Sin Murna

Aisha Yahaya, Legas

0 173

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da wasika ga takwaransa na kasar Sin, shugaba Xi Jinping, inda ya taya shi, gwamnatin kasar Sin da jama’ar kasar Sin, da kuma al’ummar kasar Sin dake Najeriya murnar shiga sabuwar shekara ta kasar Sin da aka fara daga ranar 22 ga watan Janairu.

 

 

A cikin wasikar mai dauke da sa hannun sa da kan sa, shugaba Buhari ya ce:

 

 

“A yayin bikin sabuwar shekara ta kasar Sin, wato shekarar zomo, wadda ta fara daga ranar 22 ga watan Janairu, 2023, na rubuta a madadin gwamnati da jama’ar tarayyar Najeriya domin mika sakon taya murna da fatan alheri ga mai girma Gwamna. Gwamnatin kasar Sin, da Sinawa, da al’ummar Sinawa dake Najeriya.

 

 

 

“Na yi matukar farin ciki cewa dangantakar da ke tsakanin Najeriya da kasar Sin ta tsaya tsayin daka da karfi yayin da kuke yin hadin gwiwa da gwamnatin Najeriya a ci gaban da muka samu, musamman kan ababen more rayuwa, noma, kasuwanci, wutar lantarki da tsaro. 

 

 

 

“Mai girma gwamna, ya kamata a lura da cewa, duk da rashin zaman lafiya da aka samu a duniya a shekarar 2022, kasar Sin ta ci gaba da yin tasiri mai kyau a harkokin duniya, kana ta shaida yadda aka gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 cikin nasara, wanda ya kawo kasar Sin, don shiga sabuwar tafiya don gina ƙasar gurguzu ta zamani ta kowace fuska, ƙarƙashin jagorancin ku. 

 

 

“Yayin da kuke bikin sabuwar shekara, imani na shi ne, shekarar zomo za ta kawo karin ci gaba da wadata ga Jamhuriyar Jama’ar Sin, da kara shimfida kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashenmu zuwa sabbin nasarori da ci gaba.

 

“Ina taya ku murna!”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *