Gwamnan Jijar Nasarawa a Arewa ta Tsakiyar Najeriya, Abdullahi Sule, ya ce jam’iyyar APC ta shirya tsaf domin lashe zabukan gwamnoni da na shugaban kasa da za a yi a jihar.
Gwamnan ya bayyana fatansa, a ranar Juma’a a lokacin da yake zantawa da ‘yan jaridun a fadar gwamnatin jihar, bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A cewar Gwamnan, nasarorin da ake yabawa gwamnatin jihar da kuma rabon dimokuradiyya da aka samu daga gwamnatin tarayya sun yi magana sosai kuma al’ummar jihar a shirye suke su mayar da martani.
Ya ce: “Damar mu yi nasara tana da haske. Damarmu tana da kyau duka a matakin ƙasa har da na jihohi. Mu a Nasarawa, Gwamna, Sanatoci uku ‘yan jam’iyya daya ne, kuma 20 daga cikin 24 na ‘yan majalisar dokokin jihar su ma daga APC ne.
“Mun yi iya kokarinmu ga Jihar, kuma ina ganin mutane sun yaba da hakan. Saboda haka muna ganin damarmu tana da kyau kuma mun yi imani da cewa ya kamata mu iya lashe zaben.”
Gwamnan wanda ya ce, ya je fadar gwamnatin tarayya ne domin nuna jin dadin da jihar ta yi na kafa asibitin koyarwa na jami’o’i a garin Lafia babban birnin jihar da sauran ayyuka da ake yabawa.
“A gaskiya ina nan a Villa domin ganin Shugaban kasa, don nuna jin dadinmu ga Asibitin Koyarwa da aka amince da shi a Lafiya a Jihar Nasarawa, haka nan kuma in yi masa godiya bisa tallafin da aka ba shi kan gano man da aka samu a Jihar Nasarawa.
“Kazalika muna gode masa bisa tallafin da muke ci gaba da samu musamman ta fuskar tsaro da kuma kafa cibiyar sarrafa injunan noma da aka kusa kammalawa yanzu,” inji shi.
Gwamnan ya kuma sanar da manema labarai cewa shugaban zai ziyarci jihar a ranar Asabar 4 ga watan Fabrairu, domin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Leave a Reply