Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Ekiti Ta Shawarci Manoma Shiga Tsarin Manufofin Noman koko

Aisha Yahaya, Lagos

0 128

Gwamnatin jihar Ekiti ta shawarci manoman koko da su taka rawar gani wajen tsara manufofin inganta noman koko a jihar.

 

 

 

Mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin noma da samar da abinci Mista, Ebenezer Boluwade ne ya bada wannan umarni a wani taro da kungiyoyin manoman koko da sauran masu ruwa da tsaki a garin Ado-Ekiti ranar Lahadi.

 

 

 

A cewarsa, “Hannun ƙungiyoyin a cikin tsara manufofin gwamnati zai taimaka wajen samar da darajar koko a Najeriya da Ghana da Cote D’Ivoire.”

 

 

 

Ya ce za a iya amfani da asusun ajiyar gwamnatin jihar wajen dashen shuke-shuken zamani da kuma ban ruwa a lokacin noman rani.

 

 

 

Mataimakiya ta musamman ga gwamna kan harkokin kasuwanci da zuba jari Misis Tayo Adeola, ta tabbatar da cewa jihar Ekiti na daya daga cikin manyan masu samar da kayayyaki a yankin Kudu/maso Yamma, ta jaddada cewa abubuwa sun lalace, saboda haka akwai bukatar a farfado da fannin.

 

 

 

Shugaban kungiyar manoma ta Najeriya (ALFAN), Mista Adebola Alagbada, a madadin sauran manoman koko da masu ruwa da tsaki, ya zayyana wasu kalubalen da masu noman koko ke fuskanta a jihar.

 

 

 

Ya ce, “Kalubalan sun hada da sauyin yanayi, kone-konen daji ba tare da kakkautawa ba, tsarin birane da tsarin mallakar filaye.

 

 

 

Maganganun wasu batutuwan sun hada da tallafin gwamnati ga manoman koko, wuraren ban ruwa, shiga tsakani akan lokaci, rarraba ingantattun tsirrai da sinadarai na noma.

 

 

 

Wakilan kungiyoyin manoman koko irinsu Cocoa Farmers Association of Nigeria (CFAN), All Farmers Association of Nigeria (AFAN) da kuma kungiyar masu noman koko ta Najeriya COGAN, suka halarci taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *