Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi yace Jami’ar Sufuri zata fara zangon karatun ta a cikin watan Satumba 2022.
TMinistan ya sanar da haka ne lokacin yake duba aiyyukan gine-ginen a Daura,a jihar Katsina Arewa Maso Yammacin Najeriya.
Ya yaba da yadda aikin ke tafiya,ba kamar a ziyarar baya da ya kawo ba ya taras aikin baya tafiya yadda ake bukata,ya kara da cewa sai daakayi wa Sakataren Din-din-din a maaikatar magana cewa ana bukatar a fara zangon karatu a watan satumba sannan aka maida hankali sosai.
“nayi magana da dan kwangilar kuma sunce dani akwai gini bakwai da zaa kara ginawa.kuma nayi wa sakatare na magana game da sanya idon ganin an kammala ginin. akn lokaci.
“Ina mai farin ciki da abunda na gani saboda a ziyara ta a baya banji dadin yadda irin tafiyar hawainiya da aikin ke tafiya ba. WMuna sa ran fara zangon karatu na kwasa kwasai a cikin watan satumba mai zuwa.”
Dangane da layin dogo na Kano kuwa,ministan ya kuma nuna cewa akwai kalubale matuka musamman a bangaren filin da aka bayar domin gudanar da aikin.
“AAkwai kalubale? Kwarai, akwai shi a bangaren filin da aka bayar saboda aikin amma muna sa ran shawo kan su mu da Gwamnan jihar Kano wanda shine ya bamu filin wannan itace hanyar da ta dace mu bi.”
Ya kara da cewa yabada karin umurni ga sakataren din-din-din na Maaikatar,da kanfanin dake gudanar da kwangilar CCECC, da gwamnatin Jihar kano da su gana domin samo bakin zaren warware wannan kalubale,ana sa ran kammala rahoton a ranar Juma’ar wannan mako.
Hka kuma ya duba tashar dakon kaya na kan tudu na Dala, Kano, inda ya umurci Manajan Daraktan Ahmed Rabi’u ya hanzarta kammala aikin,musamman share filin aiki domin kaddamarwa da shugabankasa zaiyi.
Ministan ya kuma kai ziyarar ban girma ga mai martaba sarkin Daura, Umar Farouk domin sanar da shi game da aikin Jamiar Sufurin da ake ginawa tare da kuma shaida masa niyyar shi na tsayawa takarar Shugaban Najeriya.
Sarkin ya yi kira ga Ministan da ya tabbatar; “an kammala Jami’ar sufuri akan lokaci.”
LADAN NASIDI
Leave a Reply