Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba da irin namijin kokarin da tsohon sakatare Janar na Majalisar Dunkin Duniya, Ban Ki-Moon wajen bada gudummowar kawo ci gaban tattalin arzikin kasar..
Shugaban ya tattauna da Ban Ki-Moon ta wayar tarho ranar Litinin tare da jaddada jin dadin shi da kuma mutumta yadda Banki -Moon ya gudanar da aiyyukan shi a UN kuma yaji dadin kiran wayar da yayi masa.
Ban Ki-Moon yaji dadin hanyoyin da Shugaban yake bi wajen shawo kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.
Hakazalika ya yaba da mukaman da ya baiwa jiga-jigan ‘yan Najeriya-Farfesa Ibrahim Gambari, Hadimin Shugaban Najeriya da kuma maaikaciyar da tayi aiki karkashin Sakatare janar na UN Mrs Amina Mohammed, wadda a halin yanzu itace Mataimakiyar Sakatare Janar da suke taka rawar gani a zauren majalisa
LADAN NASIDI
Leave a Reply