A lokacin da alumar Najeriya ke dakon zabukan shekara ta 2023, babban taron bishop-bishop na darker katolika CBCN, yayi kira ga ‘yan siyasa da su jajirce a lokacin zabuka.
Shugaban CBCN, Bishop Lucius Ugorji, shi yayi wannan kira a sakon shi na taya kiristocin Najeriya da kuma sauran takwarorin su na sauran kasashen duniya murnar ranar bukin Easter na 2022.
A cewar shi, “A dai dai lokacin da muke dakon zabukan gama gari da ake ganin na zuwa da rigingimu,muna kira ga duk wani dan Takara ya zamadan siyasa mai dattako da kuma ya dauki siyasa bada gaba ba.
“Muna kuma kira ga jama’a da su rungumi zaman lafiya.
“Saboda rikici babu abunda yake haifarwa sai tada hankalin al’uma da ba zai kawo kwanciyar hankali ga jama’a ba illa kara matsaloli ga rayuwar dan Adam.
“Baya ga fada da kasha kashen al’uma,ya kamata muyi koyi da litafin attaura inda a ciki shafi na biyu zuwa hudu yake cewa; “Ka kiyaye harshen ka” (Is 2, 4). Babu dacin rai! Babu kasha juna!”
Bishop Ugorji ya kuma tabbatar da cewa za’a samu kwanciyar hankali da zaman lafiya a Najeriya duk kuwa da halin da ake ciki “A matsayin kasa, muna bukin Easter a wannan shekara a wani irin yanayi na kunci.
“Wannan halin rashin tsaro ga rayuka da dukiyoyin Jama’a,kisan da ‘ yan taadda ke yiwa al’uma da basuji ba basu gani ba shine ya sanya shakku a zukatan mutane na rashin tabbas.
“Tattalin arziki ya shiga wani hali na haula’u da yake ci kamar wutar daji inda ya sanya miliyoyin mutane cikin hali na kakani kayi a kasar.
Wanna mumunan abu na bai wa jama’ a tsoro da damar fadin maganganu na shakku a zukatan su.”
Ladan Nasidi
Leave a Reply