A Mozambik hukumomi na ci gaba da tinkarar bala’in mamakon ruwan sama da ya haddasa ambaliyar ruwa a lardin Maputo a wannan mako.
Majiyoyin cikin gida sun ruwaito cewa akalla iyalai 2,400 ne abin ya shafa.
Ambaliyar ta shafi unguwar Matola da gundumar Boane da ke kusa da babban birnin kasar Maputo.
“Gidanmu cike suke da ruwa; ba mu da abinci da kuma inda za mu kwana, ana jan mutane daga ruwa, akwai gidaje da yawa a Caful, duk sun yi kasa da ruwa, babu wani jirgin ruwa da zai iya ceto wadannan mutane, muna neman taimako da jirage masu saukar ungulu ko kwale-kwale”, in ji Lurdes Simão Dove. wani da ambaliyar ruwa ta shafa daga gundumar Boane.
An aike da kungiyoyin ceto zuwa yankunan da abin ya shafa. Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya janyo rugujewar gidaje da dama.
“Daga jiya zuwa yau mun ceto fiye da mutane dari kuma a yau muna sa ran ceto fiye da mutane 300,” in ji Adolfo Mate, Sakatare na farko daga gundumar Boane.
Ana sa ran za a samu karin ambaliyar ruwa a lardin Maputo yayin da ruwan kogunan da suka ambaliya a Afirka ta Kudu da Eswatini ke gangarowa.
Leave a Reply