Take a fresh look at your lifestyle.

Masu Sa Kai da Agaji na Masar Sun Aika Gudunmawa Zuwa Siriya

Aisha Yahaya, Lagos

0 160

Masu aikin sa kai a Masar sun sanar da cewa,sun tattara ton 90 na taimako da za a aika zuwa yankunan da girgizar kasar ta shafa a arewacin Syria.

 

 

 

Kayayyakin sun hada da muhimman kayan abinci, barguna, tufafi da madarar jarirai.

 

 

 

“Mun shirya tattara ton biyu na gudummawa don aika (zuwa Siriya, ). Wannan ya zama mafi girma fiye da yadda muke zato, ya kai adadi mai yawa. Ton biyu ya kamata a aika a cikin akwati daya amma sun zama kwantena takwas da za a aika a cikin jirgin ruwa. Manyan motoci goma sha biyu masu lodi,  yanzu kuma wasu jirage guda uku,  kowanne zai dauki ton 20. Mun kai ton 90 a matsayin jimlar gudummawar da aka tattara – kuma muna da mai nauyin ton 120,” in ji Hassan Abdul Taawab, ma’aikacin gidauniyar Tatanaki.

 

 

 

Dimbin mutane suka halarci wajen bayar da agaji a birnin Alkahira a daidai lokacin da jama’a ke yunƙurin ba da kayayyaki da kuma taimakon agajin.

 

 

 

“Ya zuwa yanzu, girgizar kasar ta yi sanadin mutuwar mutane dubu 23. ”

 

 

Ina nan ina taimakawa da  tarin da za a tura mu Syria domin wadanda girgizar kasa ta shafa. Daya daga cikin abokaina yana tuntuɓar wannan ƙungiyar, ya taimaka wajen tattara gudummawa da yawa da muka sauke, kuma yanzu duk muna nan muna taimakawa wajen tattarawa da kuma lakafta akwatunan da za a saka a jirgin da zai wuce zuwa Siriya, in ji mai ba da agaji Renee Jian.

 

 

 

Miliyoyin ‘yan kasar Syria a arewa maso yammacin kasar na rayuwa cikin talauci, galibi suna dogaro da taimako don rayuwa tare da iyalai da dama da suka rasa matsugunansu sakamakon rikicin shekaru 12 da aka kwashe ana yi a fadin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *