A ranar Talata Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gayyaci gwamnonin jihohi 36 har da manyan hafsoshin tsaron Najeriya zuwa cin abincin bude baki a fadar shugaban kasa da Abuja.
Tun farko wasu bakin sunyi sallar Magrib tare da Shugabann kasa a Masallacin fadar shugaban kasa domn bude bakin Azumi.
A makon jiya ne dai Shauagabn kasa ya gayyaci Alkalan kotuna daban daban dake fadin Najeriya zuwa cin abincin Bude baki.
A ranar ne Shugaban kasa yayi alkawarin cewa Shugabannin gwamnati zasuci gaba da mutumta harkokin shari’a kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada domin karfafa wat sarin Demokuradiya karfi a kasar.
LADAN NASIDI
Leave a Reply