Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Najeriya ya isa Habasha don halartar taron AU

0 138

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, domin halartar taron kungiyar AU karo na 36.

 

Shugaban ya sauka a filin jirgin saman Bole, Addis Ababa a daren Alhamis da karfe 20:02 (GMT).

 

Ministan sufuri na Habasha, Dr. Alemu Sime da wasu jami’an Najeriya ne suka tarbe shi.

 

A yayin zamansa a Addis Ababa, shugaba Buhari zai halarci taruka uku na manyan jami’ai kan zaman lafiya da tsaro, sauyin yanayi da yanayin siyasa a wasu kasashen yammacin Afirka.

 

Taken taron kolin kungiyar ta AU shi ne ”Hankar da aiwatar da yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afirka”.

 

Ana sa ran shugabannin kasashe da gwamnatocin kasashen kungiyar AU su ma za su halarci taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *