Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadin da ta gabata ya aike da sako zuwa gida daga birnin Addis Ababa na kasar Habasha, inda yake halartar taron kungiyar ta AU, inda ya ce yana da cikakkiyar masaniya kan wahalhalun da wasu manufofin gwamnati suka haifar, wadanda suke nufin kawo ci gaba a kasar baki daya. sannan ya roki a kara hakuri yayin da gwamnati ke daukar matakan da suka dace domin samun sauki.
A wani faifan bidiyo na nuna goyon baya ga Bola Tinubu, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, APC a zabe mai zuwa ‘yan kwanaki kadan masu zuwa.
I am not a contestant in the coming election, but my party, @OfficialAPCNg, has a candidate in the person of Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. I am calling on all of you to vote for @officialABAT. He is reliable, a true believer in Nigeria, and he will build on our achievements. pic.twitter.com/RMHlCFuOiy
— Muhammadu Buhari (@MBuhari) February 19, 2023
Shugaban ya godewa ‘yan Najeriya da suka zabe shi ya zama shugaban kasa na wa’adi biyu, sannan ya bukace su da su zabi dan takarar jam’iyyar APC saboda “amintaccensa ne, kuma na san zai dora kan nasarorin da muka samu.”
https://web.whatsapp.com/
A cikin sakon yakin neman zaben shugaban kasar ya yi kira ga masu kada kuri’a, musamman “Sarakunan gargajiya, malaman addini da iyayenmu da su gargadi mabiyansu da na unguwanni, kada su bari wasu su yi amfani da su wajen tayar da fitina.
“Ina so in tabbatar muku da cewa gwamnati ta dauki kwararan matakan tsaro domin baiwa kowa damar fitowa ya kada kuri’arsa. Don haka ina kira ga kowa da kowa ya ba shi goyon bayan da ya dace.
“Yan uwana ‘yan Najeriya, ina so in yi amfani da wannan dama domin in sake gode muku da kuka zabe ni in zama shugaban ku a lokuta biyu.
“Ni ba dan takara ba ne a wannan zaben, amma jam’iyyata ta APC tana da dan takara a matsayin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Kamar yadda na ambata a baya, Tinubu mutum ne na gaskiya a Nijeriya, mai son jama’a da ci gaban kasarmu.
“Ina kira gare ku da ku zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Ya kasance abin dogaro kuma na yi imani zai gina kan nasarorin da muka samu.
“A karshe ina so in sake tabbatar muku da cewa ina da cikakkiyar masaniya game da irin wahalhalun da kuke fuskanta a halin yanzu sakamakon wasu manufofin gwamnati da ke da nufin kawo ci gaba ga kasa baki daya.
“Ina kira gare ku da ku kara hakuri yayin da muke daukar matakan da suka dace don saukaka wahalhalun. In sha Allahu za a samu haske a karshen ramin.”
Shugaban ya jaddada cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya nuna himma wajen ci gaban kasa da kuma rayuwar al’ummarta.
Leave a Reply