Take a fresh look at your lifestyle.

An Fara Zabe A Jihar Ebonyi

0 139

An fara kada kuri’a a unguwar Echiaba dake Ugwuachara a karamar hukumar Ebonyi a jihar Ebonyi dake kudu maso gabashin Najeriya.

Shugaban sashin kada kuri’a, Mista Georgewill Chima, ya ce komai na tafiya yadda ya kamata domin babu kalubale a yanzu. Chima ya ce tsaro na nan daram kuma ya yi farin ciki da fitowar masu kada kuri’a.

Daya daga cikin masu kada kuri’a, Mista Mbah Stanley ya ce tsarin zaben yana da inganci.

Ya godewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC bisa bullo da tsarin tantance masu kada kuri’a BIVAS.

Shima shugaban karamar hukumar Kpirikpiri mai lamba 003, Mista Igboke Emmanuel ya ce an shirya tsaf domin fara kada kuri’a a sashin sa na kada kuri’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *