Take a fresh look at your lifestyle.

Dan Takarar Shugaban Kasa A PDP Ya Kada Kuri’ar Sa

0 160

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kada kuri’arsa cikin nasara a mazabar sa dake Ajia 012 dake Jimeta Yola jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya.

Ya isa rumfunan zabe ne tare da matarshi Titi Abubakar da misalin karfe tara na safe agogon kasar, inda bayan ya kada kuri’arsa bayan minti tara.

Nan da nan bayan ya kada kuri’a, Atiku ya shaida wa manema labarai cewa yana da kwarin guiwar cewa zaben 2023 zai ba shi dama.

A halin da ake ciki dai an samu kwanciyar hankali da lumana, yanayin dandazon jama’ar da ke kewayen inda Alhaji Abubakar ya kada kuri’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *