An fara aikin tantancewa da kada kuri’a a wasu sassa na Maiduguri babban birnin jihar Borno inda rahotanni ke cewa na’urar tantance masu kada kuri’a ta Bimodal ke bada matsala.
A mafi yawan kananan hukumomin dai an fara gudanar da aikin ne a makare sakamakon rashin halartar jami’ai a wasu rumfunan zabe sannan a wasu wuraren an samu tsaiko wajen rabon kayan zabe.
Da misalin karfe 10:00 na safe a unguwar Lamisla Jambamari, Shettimari 001, a Maiduguri inda dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, ke kada kuri’arsa, da tantancewa da kuma kada kuri’a, ba a fara ba kuma babu Jami’an INEC a kasa.
A mazabar Madinatu II da ke karamar hukumar Jere inda jami’ai da kayan aiki suke a kasa, inda jama’a da dama suka fito, amma na’urar BVAS ta kasa yin aiki.
Mataimakiyar shugabar sashin, Amina Abdullahi ta ce “mutum daya ne kawai aka iya tantancewa amma ana gyara na’urar.”
Ta bayar da tabbacin cewa kowa da kowa a cikin rukunin zai kada kuri’arsa saboda za su kasance a kasa har sai an kada kuri’ar karshe.
Leave a Reply