Gwamnan jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya, Babajide Sanwo-Olu ya kada kuri’arsa a unguwar Eiyekole Ward E3 dake kan titin Adeniji Adele a tsibirin Legas.
Gwamnan wanda ya tuka kan sa zuwa sashin sa na kada kuri’a, yana tare da matarsa, Dakta Ibijoke Sanwo-Olu, da kuma ‘yan gidan sa. Gwamnan ya amince da cewa an samu ci gaba a harkar zaben, amma ya ki amincewa da isar jami’an zabe a rumfunan zabe da dama a fadin jihar a makare.
Ya ce: “An lura da atisayen yana zaman lafiya ya zuwa yanzu. Na shigo nan na gamu da fitowar mutane masu kyau. Ni da matata muka yi haquri har sai lokacin da za a ba mu izini, daga nan aka ba mu katin zaɓe don mu kada ƙuri’a ba tare da wani shamaki ba.
“Zan iya tabbatar da cewa babu wata barazana ga ‘yan kasar da suka fito domin gudanar da ayyukansu na al’umma. Na tuka mota ne daga gidan gwamnati zuwa wannan rumfar zabe; tsarin ya kasance lafiya daga lura na. Babu wani abu da ya faru ko kadan. Ina da tabbacin sakamakon da aka samu a dukkan rumfunan zabe a jihar zai nuna irin abin da muka gani idan suka fara fitowa nan da sa’o’i biyu masu zuwa.”
Sai dai Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana kwarin guiwar cewa jam’iyyar APC za ta samu nasara a karshen wannan tsari domin ya bukaci mazauna yankin da su ci gaba da zaman lafiya, yana mai rokon su da su bijirewa masu tayar da kayar baya da ke son kawo cikas a cikin tafiyar da hargitsi.
Leave a Reply