Take a fresh look at your lifestyle.

Calabar: PFN Ta Nemi A Sauya Jadawalin Zabe A Wasu Sassan Kasar

0 124

Kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria, PFN, ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, da ta sake sanya ranar zaben ranar Asabar a yankunan da aka gudanar da zaben ba bisa ka’ida ba.

Shugaban PFN a jihar Cross River da ke kudancin Najeriya, Dokta Lawrence Ekwok ya bukaci hukumar zabe da ta sake gudanar da zabukan a sassan mazabu da unguwanni da jihohin da tsarin tantance masu kada kuri’a da na’urorin BVAS suka samu matsala da/ko kuma aka ga jinkirin isar kayayyakin.

Ekwok, wanda ya kuma bayar da shawarar soke cibiyoyin da ‘yan daba suka sace akwatunan zabe, da takardan sakamako ko katin zabe, ya bayyana cewa, “muna kira ga INEC da ta soke zaben da kuma maimaita zabe a wuraren da aka hana wasu mutane kada kuri’a ko kuma inda aka yi zabe. ‘Yan bangan siyasa sun kwashe ko kuma sun lalata BVAS, akwatunan zabe da sauran kayayyakin zabe. 

“Sauran wuraren da ya kamata a soke zaben kuma a maimaita su sun hada da rumfunan zabe, unguwanni ko jihohin da takardun kada kuri’a ba su kunshi tambarin wasu jam’iyyun siyasa ba, yin hakan zai kauce wa yiwuwar zanga-zangar daga wadanda za su iya jin ba su da hakki.”

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Kuros Riba da ‘yan Najeriya baki daya da su fito baki daya domin kada kuri’ar zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha da za a yi a ranar 11 ga Maris, 2023.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *