Take a fresh look at your lifestyle.

Gobarar Maiduguri: Shugaba Buhari ya yi kira da a yi hattara

0 231

Sakamakon barkewar wata babbar gobara da ta barke babbar kasuwar Litinin ta Maiduguri, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira da a yi taka-tsan-tsan ganin yadda iska da zafi ke kara haddasa gobara a dazuzzuka da gidaje da gine-ginen jama’a da kasuwanni.

Shugaban wanda ya bayyana alhininsa kan barnar da gobarar ta afku a safiyar ranar Lahadi, ya ce addu’o’i da jajantawa al’ummar kasar na tare da ’yan kasuwa masu aiki tukuru da iyalansu wadanda aka ruwaito sun ceci ko kadan daga wutar.

Shugaba Buhari ya yaba da matakin gaggawar da gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum ya mayar kan lamarin, ya kuma ba da umarnin hada kai da hadin gwiwa tsakanin hukumomin tarayya da na jihohi domin kawo dauki ga wadanda abin ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *