Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi Na Majalisar Wakilai, Hon. Aliyu Betara ya sake lashe zabensa na kujerar dan majalisar wakilai ta mazabar Biu, Bayo, Kwaya Kusar da Shani a jihar Borno.
Betara wanda dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ya samu kuri’u 71,427 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Mohammed Ibrahim Biu na jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’u 15,514 ya zo na biyu.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, jami’in zabe na jihar Borno ya sanar da sakamakon zaben a yammacin ranar Litinin “Aliyu Betara na jam’iyyar All Progressives Congress APC bayan ya cika sharuddan doka an sake zabe shi.” Yace.
Dan majalisar ya nuna jin dadinsa ga al’ummar mazabarsa bisa goyon baya da kwarin guiwar da suka yi a tsawon shekaru da kuma yadda suka nuna jajircewarsu ga yarjejeniyar zamantakewa da ta shafe sama da shekaru goma a tsakaninsu.
“Ina so in mika godiyata ta musamman ga Allah Madaukakin Sarki da ya sanya wannan rana ta kasance. Wannan wata tafiya ce da ta faro a watannin baya bayan da suka hada kudin da suka tara don karbo min fom din tsayawa takara kuma a yau sun yi wannan alkawarin tare da kara daukar mataki ta hanyar kada kuri’a da yawa don in sake fitowa.
“Kamar yadda kuke gani, babu wani uzuri ko dalili da zai sa mutane na su yi kasa a gwiwa idan na dawo Abuja, domin a yau sun cika alkawarin da suka yi na dawo da ni, kuma lokaci na ne na cika kaina na yarjejeniyar zaman lafiya da muka shiga.
“Zan ci gaba da yin iya bakin kokarina na wakilci muradin su da sanya su a gaba a yanke shawara da ayyukana na majalisa nan da shekaru hudu masu zuwa insha Allahu.
“Ina kuma so in gode wa shugabannin babbar jam’iyyar mu ta APC bisa ci gaba da goyon baya da karfafa gwiwa a tsawon shekaru. Ina addu’ar samun nasara baki daya a zabukan shugaban kasa da na gwamnoni domin a hada kai mu samar da ingantaccen shugabanci wanda Najeriya ta cancanci,” inji shi.
Nasarar zaben da aka yi a halin yanzu shi ne sake zaben Hon. Betara zuwa majalisar don yin wa’adi na 5 mafi girma a tarihin mazabar. Dan majalisar wanda a halin yanzu yake shugabantar kwamitin kasafin kudi na majalisar, shi ma “masu sa ido suna kallonsa a matsayin daya daga cikin ‘yan takarar kujerar kakakin majalisar” mai zuwa a watan Yunin 2023.
Leave a Reply