Take a fresh look at your lifestyle.

Jihar Ebonyi; Gwamna Umahi Ya Tura Jami’an Tsaro Domin Kamo Wadanda Suka Kashe Sarki

0 253

Gwamnan jihar Ebonyi dake kudu maso gabashin Najeriya, Engr David Umahi ya tura jami’an tsaro domin kamawa tare da gurfanar da wadanda suka kashe Mai Martaba Sarki Eze Igboke Ewa da wasu yan baranda suka kashe a jiya.

Gwamna Umahi ya yi wannan yunkuri ne domin dakile ci gaba da kashe-kashe a cikin al’umma Marigayi mai martaba Igboke Ewa har zuwa rasuwarsa basaraken gargajiya ne na al’ummar Umuezekoha mai cin gashin kansa a karamar hukumar Ezza ta Arewa.

Umahi ya gargadi ‘yan siyasa da su daina tunzura matasa a kan jama’arsu ta hanyar yin wata magana da za ta iya haifar da rikici ta yadda za ta dauki rayukan mutane saboda “An sanar da ni cewa an kashe sarkin ne saboda marigayi Ewa yana goyon bayan wata jam’iyya”.

Ya kara da cewa dimokuradiyya ita ce yin zabi daban-daban.

“Dan marigayi Igboke Ewa ne ya kira ni da cewa wasu da ba a san ko su wanene ba ne suka kashe mahaifinsu, nan take na tura jami’an tsaro zuwa yankin domin kakkabo masu aikata wannan aika-aika. Na yi mamakin abin da zai iya haddasa kashe irin wannan dattijo wanda ya kai shekaru tamanin da haihuwa”.

Umahi ya kara da cewa ,“Ina rokon Allah ya duba wadanda suka kashe Sarki”.

Tsaron zabe

Gwamnan ya gargadi wasu jami’an tsaro da suka hada baki da ‘yan baranda da jam’iyyun adawa suka shigo da su domin yin magudin zabe a jihar a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

Don haka Umahi ya gabatar da koken da ya dace ga Sufeto Janar na ‘yan sanda Baba Alkali.

Ya kuma bukaci dukkan ‘yan takarar da suka fafata zabe daga jam’iyyun siyasa daban-daban da su rika neman hakkinsu a duk lokacin da suka dace maimakon yin zanga-zanga a kan tituna wadanda masu laifi za su yi awon gaba da su.

Ya godewa daukacin al’ummar Ebonyi da suka gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya cikin kwanciyar hankali a ranar Asabar da ta gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *