Take a fresh look at your lifestyle.

Kungiyar Sa Ido Ta ECOWAS Ta Ziyarci Tinubu Da Sauran ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

0 225

Jam’iyyar All Progressives Congress, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya karbi bakuncin wakilan kungiyar ECOWAS masu sa ido kan zaben, karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da tsohon shugaban kasar Ghana, Mr John Mahama a gidansa da ke Abuja.

Ziyarar tasu dai wani mataki ne na tabbatar da zaman lafiya bayan zaben.

Dattawan sun kuma gana da wasu ‘yan takarar shugaban kasa da suka hada da Peter Obi na jam’iyyar Labour (LP), Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, kungiyar ECOWAS ta bukaci a kwantar da hankula tare da yin kira ga alkalan zaben Najeriya, hukumar zabe mai zaman kanta, INEC da su bi tanadin dokar zabe ta 2022 kan tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar Fabrairu 2023.

Sun kuma bukaci INEC da ta magance matsalolin da kuma tambayoyin tsare-tsare da masu ruwa da tsaki daban-daban suka gabatar a kan babban zabe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *