Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta haramta duk wani nau’i na bukukuwa da gangamin magoya bayan jam’iyyun siyasa na nuna rashin amincewa da wanda ya yi nasara ko kuma ya fadi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka kammala a jihar.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Muhammad Jalinge kuma aka rabawa manema labarai a Kaduna.
Jalinge ya ce, duk wani abu da aka yi da gangan na karya dokar ko haifar da tabarbarewar doka da oda a kowane fanni, zai jawo fushin doka kamar yadda aka tura jami’an tsaro tare da ba da umarnin tabbatar da cikakken tsaro.
A cewar shi, ana gargadin duk wanda ke da niyyar karya wannan umarni da su daina hakan, domin rundunar ta hadin gwiwa da sauran hukumomin ‘yan uwa sun shirya tsaf domin tunkarar irin wadannan mutane kamar yadda doka ta tanada.
Ya yi kira ga jama’a da kada su yi kasa a gwiwa wajen tallafa wa jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu na tabbatar da rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Kaduna.
Leave a Reply