A yau 2 ga watan Maris ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da aikin samar da wutar lantarki a Maiduguri a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.
Ana sa ran kaddamar da aikin a ofishin TCN, tashar Baga Road a jihar.
Muryar Najeriya ta ruwaito cewa, shugaba Buhari wanda tuni ya isa Maiduguri, zai kuma jajantawa al’ummar jihar, musamman wadanda gobarar ta shafa a babbar kasuwar Litinin ta Maiduguri.
KU KARANTA KUMA: Gobarar kasuwar Maiduguri: Gwamna Zulum ya sanar da tallafin N1bn na agajin gaggawa
#HappeningToday: Presidential Commissioning of the Maiduguri Emergency Power Project (#MEPP)
Date: Thursday, 2nd March 2023
Time: 1.00pm Prompt
Venue: TCN Office, Baga Road Sub-Station, West End, Baga Road, Maiduguri, Borno StateWatch proceedings 👇https://t.co/X15jK2vC5z pic.twitter.com/4E5EPOet8M
— NNPC Limited (@nnpclimited) March 2, 2023
Leave a Reply