Take a fresh look at your lifestyle.

ECOWAS ta taya zababben shugaban Najeriyar murnar nasarar lashe zabe

0 231

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS, Commission, ta taya zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu murnar nasarar da ya samu a babban zaben Najeriya.

 

 

“A madadin Mai Girma Janar Umaru Sissoco Embalo, Shugaban Hukumar ECOWAS da gwamnatocin ECOWAS da daukacin shugabannin ECOWAS, muna so mu mika sakon taya murna ga mai girma Sanata Bola Ahmed Tinubu bisa zaben da aka yi masa a matsayin shugaban kasa na tarayya. Jamhuriyar Najeriya,” in ji Hukumar a cikin sakon taya murna.

 

 

Ya ce; “Mai girma, Janar Embalo ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su inganta zaman lafiya da kuma amfani da hanyoyin da kundin tsarin mulki ya tanada don magance duk wani koke-koke da suke da shi.”

 

 

A ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu ne aka gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *