Take a fresh look at your lifestyle.

Rundunar Tsaro Za Ta Magance Takaddamar APC Da PDP A Sokoto

Shehu Salman, Sokoto.

0 255

Wasu bayanan tsaro na sirri da gamayyar jami’an tsaro a jihar Sokoto domin tabbatar da zaman lafiya a lokuttan zabubbukan 2023 suka samu na yunkurin jan daga tsakanin manyan jam’iyun jihar na APC da PDP masu hamayya da juna suka yi na kokarin ramuwar gayya da su ke zargin junansu na hana zaɓe a wasu runhunan zaɓe da yawansu ya zarce sama da 300 a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalissar ƙasa.

Hakan ya sanya gamayyar jami’an tsaro a jihar kaddamar da wani sintiri da suka yi wa laƙabi da “KULLE-CHASS” wanda shugaban gamayyar jami’an tsaron kwamishinan ƴan sandan jihar ta Sokoto Muhammad Hussaini Gumel ya ce dole su taka wa wannan yunkurin birki gabanin zaben da lokaci da kuma bayan zaben gwamnonin da ake tunkara a ranar 11 ga watan Maris n wannan shekarar ta 2023 da mu ke ciki.
“Ba mu yadda wasu ƴan tsurarun mutane ba su kawo tashin hankali a tsakanin al’umma ba, mun ƙaddamar da wannan sintirin ne domin mu jami’an tsaro mu nuna wa duniya uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya ita ce Najeriya”

A baya dukkanin jamiyun guda biyu sun lashi takobin nuna wa juna iyakarsu ta hanyar jifar juna da munanan kalamai tare da tunzura magoya bayansu.

Hadin gwuiwar jami’an tsaron sun ce suna da wadataccin jami’ai da zasu gudanar da wannan aiki da suka hada da ƴan sanda da Soji da Ƴan sandan ciki da jami’an tsaro na farin kaya da jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi da na hukumar hana fasa ƙwauri da kuma na hana shige da fice.

Kalubalan da aka fuskanta a zaɓukan wancan makon, shuwagabannin jam’iyun APC da PDP sun zagi hukumar zaɓe da zama ummul aba’isin ruruwar rikicin na rushing kai kayan zaɓe cikin lokaci.

AK

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *