Dan takarar gwamna na jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP a jihar Ebonyi, Dr Sunday Adolawam ya karyata maganar cewa ya ruguza tsarin jam’iyyarsa domin marawa dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressive Congress APC, Mista Francis Nwifuru a zabe mai zuwa.
Dr Adolawam ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Mista Victor Uraku a Abakaliki babban birnin jihar, kudu maso gabashin Najeriya.
Shugaban kungiyar matasan Izhi Nnodo na kasa, Ben Nwovu ya ce Mista Adolawam ya ruguje tsarinsa a takarar Gwamna domin marawa dan takarar APC baya.
Sanarwar ta ce; “Majalisar yakin neman zaben Allah na jam’iyyar NNPP a jihar Ebonyi ta yi kakkausar suka ga kalaman Ben Nwovu…Irin wadannan ikirari na hannun barna ne da ke da burin ganin sun zubar da farin jinin Dr Adolawam a matsayin dan takarar gwamna a jihar Ebonyi. .”
Ya ce; “Dr Adolawam ya jajirce wajen kyautata rayuwar al’ummar jihar Ebonyi.
Dr Adolawam ya ce; “Bari in bayyana cewa, ba ni da kuma ba zan yi murabus ga kowa ba. Na kuduri aniyar tsayawa takarar gwamna a jihar Ebonyi, kuma ina da yakinin samun nasara.
“Yakin neman zabe na ya ginu ne a kan ginshikin gaskiya, rikon amana, da shugabanci na gari, kuma ina samun goyon bayan mutanen da suka yi imani da tunanina na inganta jihar Ebonyi.”
Don haka, ya yi kira ga al’ummar Jihar Ebonyi da su fito gaba daya domin kada kuri’arsu, domin ganin Jihar ta zama ta daya a Najeriya.
“Dukkan mutanen Ebonyi za a ba su iko daban-daban, saboda haka talauci ba zai da wani matsayi a cikin jihar,” Dr Adolawam ya yi alkawari.
Leave a Reply