Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajantawa kan hatsarin da jirgin kasa da kuma motar ma’aikatan jihar Legas da ake kira Bus Rapid Transit (BRT) suka yi a ranar Alhamis a unguwar Shogunle da ke Ikeja a jihar Legas.
Shugaba Buhari ya ce:
“Hatsarin da ya afku a mashigar da jirgin kasa da kuma motar bas din ma’aikatan BRT abin damuwa ne kuma abin bakin ciki ne matuka. Ina yi wa wadanda suka rasu addu’a, da samun sauki ga wadanda suka jikkata.”
Shugaban ya yabawa hukumomin jihar Legas da hukumomin bada agajin gaggawa da suka gaggauta shiga aikin agaji.
Leave a Reply