Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan ya shafe sama da makonni biyu a garin Daura na jihar Katsina.
Shugaban ya samu tarba ne a bangaren shugaban kasa na filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a yammacin ranar Litinin da ta gabata ta hannun shugaban ma’aikatan fadar sa, Farfesa. Ibrahim Gambari da Ministan Babban Birnin Tarayya, Mohammed Bello.
Shugaban na Najeriya ya kwashe sama da makonni biyu a garin Daura, inda ya bar Abuja ranar 23 ga watan Fabrairu domin halartar zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Ana sa ran zai koma cikin mako guda don kada kuri’arsa a zaben gwamna, wanda aka shirya yi a ranar Asabar 18 ga Maris 2023.
Leave a Reply