Take a fresh look at your lifestyle.

Saura Kiris Al’umar Jihar Kaduna Su Yanke Hukunci: Suleiman Hunkuyi

Musa Aminu, Abuja

0 216

Yayin da ya rage kwanaki kalilan a gudanar da zaben Gwamnanoni da na Yan majalisun dokokin jihohi a Najeriya, an yi kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta a kasar da ta tabbatar ta dauki matakan gyara kura kuren da suka faru a lokacin zaben shugaban kasa da na Yan majalisun dokokin tarayya Najeriya, musamman ma yadda aka wofantar da logon jam’iyyar su ta NNPP a cikin jerin jam’iyyun da masu zabe zasu Kada kuri’arsu yayin zaben.

Wannan Kiran ya fito ne daga bakin dantakarar gwamnan jihar Kaduna dake Arewa maso yammacin Najeriya karkashin tutar jam’iyyar New Nigerian People’s Party NNPP Sanata Suleiman Othman Hunkuyi.

Kazalika, Sanata Hunkuyi ya bukaci masu zabe, musamman a jihar Kaduna da su guji zaben dantakara saboda wani dan abunda bai taka kara ya karya ba, kama daga kayan abinci da ba zai kashe kishi ba da kuma kudade da wasu ke yaudararsu da shi.

Bugu da Kari, dantakarar na jam’iyyar NNPP ya nuna takaicinsa bisa yadda wadansu ke sanya kabilanci da amfani da addini domin cimma bukatunsu, ya kuma bukaci Malamai da su shiga taitayinsu kan abunda ya shafi amfani da su da wadansu Yan siyasa ke yi ta hanyar rarraba kan al’umma domin ganin hakar su ta cimma ruwa.

Sanata Suleman Othman Hunkuyi ya kara da cewa al’umar jihar Kaduna sune alkalai Kuma nan da Yan kwanaki kadan zasu yanke hukunci akan abunda ya dace a gare su, inda ya ce ya nada yakinin cewa duk abunda suka zaba shi za a basu.

A karshe, dan siyasan ya ja hankalin al’umma, musamman matasa da su guji ta da zaune tsaye a lokacin zaben da ma bayansa domin zaman lafiya shi ne babban burin duk wani dan kasa na gari.

 

AK

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *