Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar Zartaswa Ta Amince Da Naira Biliyan 15 Na Hanyar Da Ta Hada Gadar Neja

0 113

Majalisar zartaswar Najeriya ta amince da kashe zunzurutun kudi har Naira biliyan 15 domin gina hanyar da ta hada babbar hanyar Benin zuwa Asaba zuwa gadar Neja ta biyu.

 

 

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnatin jihar a karshen taron majalisar zartarwa ta tarayya a ranar Laraba.

 

 

Ya ce kammala hanyar zai taimaka wajen cimma burin bude gadar kafin gwamnati mai ci ta bar mulki a watan Mayu.

 

 

“Ministan ayyuka ya gabatar da takardar neman amincewar bada kwangilar gina hanyar da ta tashi daga babban titin Benin zuwa Asaba da ake da ita domin tunkarar titin da ta hada da gadar Neja ta biyu a jihar Delta.

 

 

“Kamar yadda kuka sani gwamnati ta kuduri aniyar kaddamar da gadar Neja ta biyu kafin karewar wannan gwamnati. Za mu iya gaya muku cewa gadar da kanta an Gina ta sosai amma kwangilar da aka bayar a yau, duk da cewa an fara aikin kafin yanzu, hakika shine haɗa ƙarshen Asaba-Benin zuwa sabuwar gada.

 

 

“An bayar da kwangilar ne ga Julius Berge akan kudi naira biliyan 15. Sun fara aikin amma sun ce ya dace su na da kwangila. Muna ba ku tabbacin cewa hanyar za ta kare cikin lokaci mai kyau domin mu kaddamar da gadar Neja-Bridge ta biyu,” inji shi.

 

 

Mohammed ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da kashe Naira Biliyan 16 a matsayin karin kudin aikin titin Suleja zuwa Minna a Jihar Neja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *