Karamar hukumar Calabar ta kudu ta samu raguwar fitowar masu kada kuri’a a zaben gwamna da ‘yan majalisar jiha da ke ci gaba da gudana a jihar.
Duk da cewa mazauna karamar hukumar sun bi umarnin hana zirga-zirgar da gwamnatin Najeriya ta yi, amma an ga masu zabe a rumfunan zabe daban-daban ba su da yawa.
An lura cewa mutane kalilan ne suka fito domin kada kuri’a a karamar hukumar da ke da yawan jama’a; ba kamar a unguwar Calabar Municipality ba inda aka fara kada kuri’a tun karfe 8:30 na safe a galibin unguwannin saboda kayan sun isa da wuri.
Masu jiran zabe
Cibiyoyin jefa kuri’a da aka ziyarta a gundumar 12 ta Calabar ta kudu, karamar hukumar ta nuna a kusa da runfunan da ba kowa a cikinsu yayin da jami’an hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ke jiran masu kada kuri’a.
A rumfar zabe mai lamba 044, a Ekpo Abasi, daya daga cikin masu kada kuri’a, Mista Charles Obo ya bayyana cewa tun karfe 8:30 na safe an fara tantancewa da kada kuri’a amma mutane kadan ne suka samu damar kada kuri’a.
Obo ya jaddada cewa kila yawan fitowar masu kada kuri’a ya samo asali ne sakamakon abin da ya kira tauye hakkin masu kada kuri’a a zaben shugaban kasa da ya gabata lokacin da yawancin Bimodal Voter Accreditation Systems, (BVAS) suka gaza.
A cewar wata mai kada kuri’a, Misis Esther “Mutane ba sa fitowa saboda suna ganin ba za a kirga kuri’unsu ba saboda abin da ya faru makonni uku da suka wuce.”
Wani mai jefa kuri’a, Mista Reuben Ephraim kuma ya ce “Ina ganin da wuri ne, har yanzu mutane za su fito su kada kuri’unsu”.
Leave a Reply