Zababben mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya kada kuri’arsa a rukunin sa Alhaji Kukawa (PU023), Lamisala Jambamari ward a Maiduguri Metropolitan Council a jihar Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya.
Zababben mataimakin shugaban kasar ya isa rumfar zabe inda ya kada kuri’arsa da karfe 11:00 na safe.
Idan dai ba a manta ba a baya Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum da mataimakinsa Umar Usman Kadafur ne suka kada kuri’a a rumfar zabensu.
()
Leave a Reply