Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamna Tambuwal Da Mataimakin Sa Sun Jefa Kuri’a; Sun Kuma Nuna Gamsuwa Da Tsari

0 145

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da mataimakinsa, Manir Dan’iya, sun kada kuri’unsu a zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kada kuri’a, Gwamnan ya yabawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da jami’an tsaro bisa tabbatar da yanayi na lumana don gudanar da zaben.

Sai dai ya bukaci INEC da ta gaggauta tura sakamakon zaben gwamna ta hanyar na’ura mai kwakwalwa, domin tabbatar da sahihancin zaben a jihar.

Gwamna Tambuwal ya kuma yi kira ga masu zabe da su ci gaba da baiwa jami’an INEC da jami’an tsaro hadin kai domin samun nasarar gudanar da zaben.

A nasa bangaren, Manir Muhammad Dan’iya, mataimakin gwamnan jihar ya nuna jin dadinsa da shirye-shiryen da INEC da sauran masu ruwa da tsaki suka yi.

Ya bayyana cewa an samu ci gaba sosai a wannan zabe idan aka kwatanta da abin da aka gani a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a watan jiya.

Dan’iya ya ce yana da yakinin cewa jam’iyyarsa ta PDP ce za ta lashe dukkan zaben jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *