Take a fresh look at your lifestyle.

Kungiya Ta Yabawa ‘Yan Najeriya Bisa Yadda Aka Gudanar Da Zabe Cikin Lumana

0 205

Kungiyar ‘yan jarida mai zaman kanta a karkashin shirin Community Initiatives to Promote Peace (CIPP) ta yabawa ‘yan Najeriya bisa yadda aka gudanar da zaben gwamnoni da na majalisun jihohi cikin kwanciyar hankali.

A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Litinin, shugaban kungiyar, Ibrahima Yakubu, ya yabawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), bisa raba kayan zabe a kan lokaci. Kungiyar ta kuma yabawa Jihohi da Gwamnatin Tarayya bisa yadda suka samar da isasshen tsaro a fadin kasar nan a lokacin zabe.

Ya bayyana jin dadinsa kan zaben gwamnoni da na majalisun jihohi da aka kammala a yanzu yana mai bayyana shi a matsayin mafi kyawu a tarihin Najeriya.

Yayin da ya yi kira ga ‘yan takarar da suka sha kaye a zaben da su karbe shi da idon basira don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, kungiyar ta kuma yi gargadi kan yada labaran karya a shafukan sada zumunta tana mai cewa “ya kamata ‘yan kasa su yi taka-tsan-tsan da labarai a Facebook, twitters. Instagram, WhatsApp da dai sauransu,” in ji shi.

Ya yabawa kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya bisa bude dakunan da suka shafi yanayi a lokacin zabe da kuma bayan zabe, ya kuma yi kira ga ‘yan kasar da su rika samun labarai a ko da yaushe daga amintattun kungiyoyin yada labarai.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *