Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar Wakilai Ta Yi Taron Jin Ra’ayin Jama’a Kan Dokar Kafa Hukumar Kula da Al’majirai

Abdulkarim Rabiu, Abuja

442

Majalisar Wakilan Najeriya ta gudanar da taron jin ra’ayoyin jama’a akan kudirin dokar kafa – hukumar kula da almajirai da yaran da basu damar shiga makaranta ba da nufin rage gararanbar yaran akan tituna.

Matsalar gararanbar al’majirai da yaran da basu samu damar shiga makaranta ba na ci gaba da kasancewa babban kalubalen dake haifar da matsaloli na rashin ilimi, talauci da tsaro musanman a yankin arewa masu yammacin Najeriya.

A bisa wannan dalilin ne ya sa gwamnatocin da suka gabata suka yi ta kokari domin ganin sun samar da kyakkyawan tsari na ilimin tsangaya ta yadda zai yi daidai da tsarin ilimi na zamani wanda kuma ake ganin zai taikama wajen rage matsaloli daban daban da rashin ilimin ke haifarwa a kasar.

A ci gaba da wannan kokari ne Kuma, Dan Majalisar Wakilai daga Jihar Sokoto, Dakta Shehu Balarabe Kakale ya dauki nauyin wani kudirin doka da ya nemi kafa hukumar da zata kula da ilimin tsangaya da yaran da basu samu damar shiga makaranta ba ta yadda za a samar da kyakkyawan tsarin ilimi da zai magance matsalar jahilci, da samar da ayyukan yi ga matasa.

Yanzu haka dai kudirin ya zartar karatu na biyu Kuma ya samu gagarumin goyan baya daga masu ruwa da tsaki da suka halarci taron Jin ra’ayoyin jama’a da Majalisar ta gudanar ranar talartan nan. Kamar yadda Shehu Kakale ya yi Karin haske.
“gyaran tsarin karatun allo da almajirci da inganta shi , shi ne zai samar wa da Najeriya arziki, shi zai sa mutanene su shiga cikin kasuwanci , fasaha da kere-kere da samar wa da Najeriya kudaden shiga fiye da yadda a ke tsammani. Wannan tsarin na gina al’umma ne sannan kuma gwamnati za ta Kara samun kudaden shiga saboda za a gina al’umma, kowa ya dogara da kanshi, masana’antu su tashi, noma ya habbaka sannan a sami tsaro” In ji Shehu Kakale

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa Farfesa Mohammed Shafi’u Abdullahi, tsohon shugaban hukumar kula da Larabci da karatun islamiyya, wanda na daya daga cikin wadanda suka goyi bayan kudirin ya ce “yin haka wajibi ne ga gwamnati domin hakki ne na ko wane yaro a Najeriya ya samu ilimin da ya kamata, musanman akalla ilimin da dai gaza na firamare ba. Saboda haka mu muna goyan bayan Wannan ra’ayi na kirkirar Wannan hukumar wadda zata kula da yara wadanda ba su da galihu”

Ita ma shugabar kungiyar dake fafutukar inganta rayuwar al’ummar Najeriya Dakta Fatima Goni, wadda har ila yau na daya daga cikin wadanda suka bada gagarumar gudunmawa a kokarin samar da dokar kafa hukumar ta kula da al’jimarai, ta ce dalilin da ya suka goyi bayan wannan doka shi ne kungiyarsu tana da ra’ayi na taimaka wa gajiyayyu musanman al’majirai.

Shugabar kungiyar ta bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunta Hajiya Riskatu Abdulaziz.
” Tun da dadewa mu ma mun bukaci samar da irin wannan doka ta kafa hukumar, dalili da cewa kungiyarmu muna da son taimaka wa gajiyayyu musanman al’majirai shi ya sa muke farinci da marhabin da wannan abu”. In ji Dakta Fatima Goni

To saidai duk da wannan mahinmanci da kafa hukumar ya ke da shi, ma’aikatar ilimi ta tarayya bata goyi bayan kudirin dokar ba. To ko menene Dalali? Har ila yau Hon. Shehu Kakale ya ce; “dalili kawai shi ne ta ce wai gwamnatin bata da isassun kudade, kudaden dake aljihunta za su Kara tsiyayewa”

Taron dai ya samu halartar masu ruwa da tsaki kan harkar ilimi da suka hada da jama’in gwamnati, da Malaman addini da Kuma saraukunan gargajiya da sauransu.

Abdulkarim Rabiu

Comments are closed.