Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabbin sakatarorin dindindin guda shida a ma’aikatan gwamnatin tarayya.
Nadin ya biyo bayan tsarin zaben da aka gudanar kwanan nan.
Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya Dr Folasade Yemi-Esan ce ta bayyana hakan a Abuja, babban birnin Najeriya.
Sakatarorin dindindin da na su
Jihohin da suka fito sune kamar haka;
Mahmud Kambari – Borno
Esuabana Asanye – Cross River
Lamuwa Ibrahim – Gombe
Yakubu Kofar-Mata -Kano
Oloruntola Michael -Ogun
Richard Pheelangwah –Taraba
Nan gaba kadan ne za a bayyana ranar da za a rantsar da kuma tura sabbin wadanda aka nada.
Leave a Reply