Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Madina na kasar Saudiyya a yayin da ya fara ziyarar aiki ta kwanaki takwas a kasa mai tsarki.
Bayan isowarsa, Mataimakin Gwamna Sa’ud Khalid Al-Faisal ne ya tarbe shi.
Shugaban ya kai ziyara tare da yin addu’a a masallacin Annabi mai alfarma da yammacin ranar Talata tare da gaishe da Annabi Muhammad (SAW) da sahabbansa guda biyu.
A kofar Masallacin Annabi mai alfarma, shugaban ya samu tarba daga jami’ai da dama.
Leave a Reply