Hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA, ta sake karbar wasu ‘yan Najeriya 107 da suka makale a birnin Tripoli na kasar Libya.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba a Legas.
Hukumar NEMA ta ce wadanda suka dawo sun isa filin jirgin saman Murtala Muhammad, Cargo Wing, Ikeja, da yammacin ranar Talata a cikin jirgin Al Buraq Air Boeing 737-800 mai lamba 5A-DMG.
https://von.gov.ng/107-more-nigerians-return-from-libya/
Wadanda aka dawo da su sun hada da maza 53, mata 52 da jarirai biyu.
Darakta Janar na NEMA, Mista Mustapha Ahmed ne ya karbi bakuncin wadanda suka dawo a madadin gwamnatin tarayya a hukumance.
Kungiyar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya tare da goyon bayan abokan hulda na kasa da kasa, tana taimakawa ‘yan Najeriya da ke makale a Libya domin komawa gida tun shekarar 2017.
Leave a Reply