Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ne ke jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya, a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja.
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folashade Yemi-Esan na daga cikin wadanda suka halarci taron.
Sauran sun hada da ministocin yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, kudi, Zainab Ahmed, harkokin mata, Pauline Tallen, cikin gida, Rauf Aregbesola; Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; Kimiyya da Fasaha, Olorunimbe Mamora; Noma, Mohammed Abubakar; Lafiya, Dr Osagie Ehanire; da Wasanni, Sunday Dare da sauransu.
https://twitter.com/VillaUpdatesng/status/1648630994281406464?ref_src=twsrc%5Etfw%7Ctwcamp%5Etweetembed%7Ctwterm%5E1648630994281406464%7Ctwgr%5Ec594630ae1feb7c559ffc4b94cf4fa36c70e05ca%7Ctwcon%5Es1_&ref_url=https%3A%2F%2Fvon.gov.ng%2Fvice-president-osinbajo-presides-over-cabinet-meeting-3%2F
A halin da ake ciki kuma, a yau ne ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo Abuja, bayan wata ziyarar aiki ta kwanaki takwas a kasar Saudiyya, inda ya gudanar da aikin Hajjin karama, wanda aka fi sani da Umrah.
Ya kuma ziyarci Masallacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam tare da zagaya wajen baje kolin tarihin rayuwar Manzon Allah a birnin Madina na duniya inda ya kai kara domin a samu daidaiton fahimtar addinin Musulunci ta hanyar gyara kuskuren fahimtar addinin da aka dade shekaru aru-aru.
Leave a Reply