Fadar shugaban kasa ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lura da hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke na mayar da Sanata Ifeanyi Ararume a matsayin shugaban rikon kwarya na kamfanin mai na Nigeria National Petroleum Company Limited (NNPCL).
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina, a wani sako da ya fitar ranar Laraba, ya ce gwamnati za ta daukaka kara kan hukuncin.
“Yayinda har yanzu ofishin babban mai shigar da kara na tarayya/Ministan shari’a bai samu kwafin hukuncin ba, shugaban kasa ya tabbatar da cewa za’a bi tsarin shari’a, kuma NPL ta riga ta dauki matakin daukaka kara,” in ji shi. yace.
Adesina ya kara da cewa gwamnatin da ke yanzu tana mutunta doka, kuma ba za a yi wani abu a wajenta ba don warware matsalar.
Ya ce saboda haka shugaba Buhari yana neman a kwantar da hankula daga dukkan bangarorin da abin ya shafa.
Leave a Reply