Take a fresh look at your lifestyle.

UBEC Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Zamanantar Da Yanayin Koyo Da Koyarwa A Makaratun Firamare

Musa Aminu, Abuja

0 232

Hukumar kula da ilmin bai daya ta Najeriya wato UBEC ta sha alwashin ci gaba da zamanantar da yanayin koyo da koyarwa a makaratun firamare da kamar sakandire dake fadin kasar baki daya.

Shugaban kwamitin gudanarwar hukumar ko kuma chairman board of Directors a turance, Farfesa Adamu Kyuka Usman shi ne ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da Muryar Najeriya dangane da cikarsa shekaru uku kan wannan mukamin.

Farfesa Adamu kyuka Usman ya bayyana cewa cikin shekaru uku da ya kwashe a matsayin shugaban gudanarwar daraktocin hukumar kula da ilmin bai daya, wato UBEC, sun sami nasarar zamanantar da harkokin koyo da koyarwa inda zamantar da littafen da aka buga shekaru aru-ru da suka gabata ta yadda zasu yi daidai da daliban wannan lokaci, sun kuma kawo sauyi kan yadda daraktocin humukar ke gudanar da taron masu ruwa da tsaki na lokaci bayan lokaci.

Kazalika, Shehin malamin ya kara da cewa sun bijiro da harkar koyo da koyarwa da harshen uwa domin ganin Najeriya ta bi sahun kasashen da suka ci gaba
InsertFarfesa kyuka Usman wanda har ila yau masani ilmin dokoki a Najeriya, yace akwai doki dake kawo tsaiko a wasu fannoni a kasar, ciki har da bangaren ilimi, hakan ta sa suka kwaskware wasu daga cikin dokokin hukumar ta UBEC.
Sai dai ya bayyana yadda gwamonin wasu jihohi ke neman zame hannunsu daga kula da makarantun firamare din jihohinsu da zummar dora alhaki ga hukumar kula da ilmin bai daya ta Najeriya kacokan a matsayin babban kalubale da hukumar ke fuskanta.

 

Abdulkarim Rabiu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *